1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe dalibai da malamai a Siriya

October 27, 2016

Akalla yara kananan 'yan makaranta uku suka mutu yayin da wasu 14 suka jikkata a wani mumunan harin makaman roka da ake zargin 'yan tawayen Siriya sun kai a kan makarantar gwamnati da ke yammacin birnin Aleppo.

https://p.dw.com/p/2Rms2
Syrien Aleppo Bergung Verletzte nach Luftangriff Kinder
Hoto: picture alliance/AA/A. Al Ahmed

Kungiyoyin da ke sa ido a Siriya sun ce 'yan tawaye na amfani da makaman roka a yayin mai da martanin kan sojojin gwamnati da na kawancensu na Rasha da ke kaddamar da sumamae a yankunansu, wanda hakan ke yin mumunar Illa ga rayuwar fararen hula da ke yammacin birnin na Aleppo.

Wannan sabon harin dai na zuwa ne kwana guda bayan da hukumar kula da kanana yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ta ce ta samu rahotannin da ke zargin jiragen kawancen yakin Siriya da na Rasha sun kashe kananan yara 22, tare da hallaka malamai da dama a wani makaranta da ke lardin Idib. To sai dai Rasha ta yi Allah wadai da wannan zargi.