An kashe Bajamushe daya a Sagamu na Ogun | Labarai | DW | 27.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe Bajamushe daya a Sagamu na Ogun

Wasu 'yan bindiga sun hallaka wani Bajamushe guda sannan suka yi awon gaba da karin wani a garin Sagamu da ke jihar Ogun a kudu maso yammacin tarayyar Najeriya.

Masu aiko da rahotanni suka ce 'yan bindigar sun bude wuta ne kan motocin da Jamsuwan ke ciki, wanda suke yi wa kamfanin nan na Julius Berger aiki a kasar a ranar Jumma'ar da ta gabata kamar yadda mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar ta Ogun ta shaida wa manema labarai.

Mai magana da yawun kamfanin na Julius Berger a Najeriya ya tabbatar da wannan labarin kuma ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya da ta bayyana cewar ita ce ke da alhakin kisan Bajamushe da kuma sace abokin aikinsa.

Kame 'yan kasashen waje da nufin neman kudin fansa abu ne da ke zaman Jampa a Jos a kudancin tarayyar ta Najeriya.