An karya yarjejeniyar tsagaita wuta a Yaman | Labarai | DW | 15.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An karya yarjejeniyar tsagaita wuta a Yaman

'Yan tawayen Houthis sun kashe mutane guda bakwai a cikin wasu hare-haren da suka kai a yankin gabashi na ƙasar.

Wakilai na gwamnatin Yaman da na yan tawaye na ci gaba da tattaunawa da zumar samar da sulhu a ƙasar Suizeland a ƙarƙashin jagorancin Majalisar Ɗinkin Duniya.Sai dai rahotannin da ke zuwa mana daga Yaman na cewar 'yan tawayen Houthis sun kashe farar hula guda bakwai a cikin wasu ruwan bama-bamai da suka yi a yau duk kuwa da yarjejeniyar tsagaita wutar da aka saka hannu a kanta.

Tun a cikin watan Maris da ya wuce ake gwabza kazamin fada tsakanin dakarun gwamnati masu samun goyon bayan Saudiyya;da kuma mayaƙan 'yan tawaye Houthis 'yan Shi'a masu samu tallafi ƙasar Iran.