An karya yarjejeniyar tsagaita wuta a Siriya | Labarai | DW | 04.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An karya yarjejeniyar tsagaita wuta a Siriya

Wasu jiragen sama na yaki wadanda kawo yanzu ba'a tantance asalinsu ba, sun kai hare-hare guda biyu a kusa da birnin Douma cibiyar 'yan tawayen Siriya..

Rahotanni daga kasar Siriya na cewa a karo na farko tun bayan soma aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta a yakin Siriya an samu abkuwar wani hari wanda ke zama keta haddin wannan yarjejeniyar.

Kawancan kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasar ta Siriya na OSDH ya ruwaito cewa wasu jiragen sama na yaki wadanda kawo yanzu ba a kai ga tantance asalinsu ba sun kai wasu hare-hare guda biyu ta sama a kusa da birnin Douma cibiyar 'yan tawayen Siriyar da ke a Gabashin birnin Damas inda suka halaka mutun daya.

Sai dai kwamitin gudanarwa na majalisar kungiyoyin 'yan tawayen na birnin na Douma ya ce yana kyautata zaton jiragen da suka kai harin na kasar Rasha ne. Yau mako daya kenan da da yarjejeniyar tsagaita wutar ta soma aiki ba tare da wani bangare ya karya ta ba kafin wannan hari na baya-bayan nan.