An kara dakarun Monusco a gabashin Kwango | Labarai | DW | 06.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kara dakarun Monusco a gabashin Kwango

Rundunar Majalisar Dinkin Duniya ta Monusco a Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango, ta sanar da aike wasu karin dakarunta a yankin Beni da ke gabashin kasar.

Hakan na zuwa ne bayan wani harin kwonton bauna da ya yi sanadiyar rasuwar dakarunsu biyu dukanninsu 'yan kasar Tanzaniya. Da yake magana kan wannan batu, kakakin rundunar ta Monusco Félix Prosper Basse, ya ce sun tura wasu dakaru ne na musamman domin kawo agaji ga dakarunsu da suka fuskanci wannan matsala a yankin na Beni, inda ya kara da cewa babban komandan sojojin na Monusco Janar Carlos Alberto dos Santos Cruz, wanda dan kasar Brazil ne, zai kai ziyara a garin na Beni domin jagorantar ayyukan dakarun, wanda a cewarsa dole ne sai an dauki tsauraran matakai kan mayaka 'yan tawaye da ake zargi 'yan kasar Uganda ne masu adawa da gwamnatin shugaba Yoweri Museveni, wadanda ke gabashin kasar ta Kwango tun daga shekara ta 1995.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Pinado Abdu Waba