An kammala zaben shugaban kasa a Uganda | Labarai | DW | 23.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kammala zaben shugaban kasa a Uganda

A ƙasar Uganda an kamalla tagwayen zaɓe, na shugaban ƙasa, da na yan majalisun dokoki.

Wannan shine karo na farko ,tun shekaru 26 da su ka wuce, da ƙasar Uganda, ke shirya zaɓe, bisa tafarkin demokraɗiyya.

A baki ɗaya, mutane million10 da rabi, za su zaɓi ɗaya daga yan takara 5, da su ka shiga gwaggwarmayar neman shugabancin wannan ƙasa.

Yan takara sun haɗa da shugaban mai ci yanzu ,Yoweri Museveni, da ke kan karagar mulki tun shekara ta 1986, wato shekaru 20 kenan ,da su ka shuɗe.

ƙiddidigigar neman jin ra´ayin jama´a , ta bayyana cewar shugaba Yoweri za shi tazarce.

A nasu gefe,tunni yan adawa sun fara ƙorafin shirya magudi.

Ya zuwa yanzu, rahotanin daga Kampala baban birnin kasar, sun shada cewar zaɓen ya wakana lami lahia, duk da yan matsaloli da a ka fuskanta, a lokacin kampen.

Saidai, ruwan sama kamar da bakin kwarya da a ka sheka a wasun yankunan, da kuma yan matsaloli nan da cen na kayan aiki,sun sa jinkiri a wasu runhunan zaɓe.

A na sa ran fara samun sakamako, tun gobe juma´a.