An kammala taron kolin kasashen nahiyar Amirka | Labarai | DW | 06.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kammala taron kolin kasashen nahiyar Amirka

An tashi baram-baram a taron kolin kasashen nahiyar Amirka ba tare da cimma tudun dafawa ba dangane da shirin kafa wani yankin ciniki maras shinge. Shugabannin kasashe 34 da suka halarci taron kolin a wurin shakatawa na Mar del Plata dake kasar Argentina sun kasa cimma wata yarjejeniya tsakanin su. To sai dai bayan ja-in-ja mahalarta taro sun amince da wata yarjejeniya wadda a ciki suka bayyana bambamce bambamcen dake tsakanin su. Wata sanarwar bayan taro da suka sanyawa hannu, shugabannin sun nuna aniyar su ta yaki da matsalolin talauci a nahiyar Amirka baki daya. Shugaban Amirka GWB ya ba da shawarar kirkiro wani yankin ciniki da kowa ka iya shiga ciki ba tare da wata tsangwama ba. To sai dai kasashe kamar Brazil da Argentina da kuma Venezuella sun nuna adawa da wannan shawara musamman saboda fargabar wani babakeren Amirka a nahiyar.