An kammala shirye-shiryen zaben Zimbabwe | Labarai | DW | 30.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kammala shirye-shiryen zaben Zimbabwe

Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya yi alkawarin rungumar kaddara muddin ya fadi a zabe a wannan Laraba.

A hannu daya kuma shugaban ya yi watsi da rade-radin yuwuwar tafka magudi. Shugaban ya bayyana haka yayin taron manema labarai da ya gudanar da yammamcin ranar Talata.

An kammala duk shirye-shiryen gudanar da zaben, inda za a yi fafatawa mai zafi na neman shugabancin kasar, tsakanin Shugaba Robert Mugabe da Firaminista Morgan Tsvangirai.

An jibge jami'an tsaro cikin yankunan da ake fargabar samun tashin hankali. Kafofin yada labaran gwamnati sun ce, an dauki matakin domin kauce wa duk wani tashin hankali da za a iya samu lokacin zaben.

Duk manyan jam'iyyun siyasar kasar biyu, wato ZANU-PF da MDC, na ikirarin yuwuwar samun nasara. Mugabe ke mulkin kasar ta Zimbabwe tun bayan samun 'yancin kai shekaru 33 da suka gabata, daga Turawan mulkin mallakan Birtaniya.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal