1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kammala shirin zabe a Gunea Bissau

April 11, 2014

A wannan lahadin ce al'ummomin Guinea Bissau ke gudanar da zaben shugaban kasa da na wakilan majalisa, a kasar da ke fama da matsaloli.

https://p.dw.com/p/1Bgj9
Wahlkampagne in Guinea-Bissau
Hoto: DW/Braima Darame

A wannan lahadin ce al'ummomin Guinea Bissau za su kada kuri'unsu a zaben shugaban kasa da 'yan majalisa, wanda ake fata zai dawar da zaman lafiya a wannan kasa da ke fama da matsalolin fataucin kwayoyi da juyin mulkin sojoji.

Tun daga shekara ta 2012 ne dai kasar ta yammacin Afrika ta ke karkashin gwamnatin rikon kwarya da ke da goyon bayan sojoji, baya ga talauci da fataucin paudar iblis da ke ruruta rashawa.

Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama, ya yi fatan cewar zaben zai tsame Guinea Bissau daga matsalolin da suka dabaibayeta.

Ya ce" wannan ba abu ba ne mai sauki, kasancewar tsarin demokradiyya bai tsaya ga gudanar da zabe kadai ba, ainihin tafiyar za ta fara ne bayan zaben, hada kai domin aiki tare, shi ne zai tabbatar da nasarar dorewar wannan tsari.

A watan Afrilun bara ne dai Amurka ta samu jagoran kifar da mulkin 2012 Antonio Indjai da laifin fataucin kwayoyi da sayar da makamai wa mayakan sa kai na kasar Kolumbiya, sai dai har yanzu ba'a gurfanar da shi ba, kuma ya na ci gaba da zama a kasar ta Guinea Bissau.

Mawallafiya : Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Umaru Aliyu