An kammala kada kuri′a a zaben gama gari a Zambiya cikin lumana | Labarai | DW | 11.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kammala kada kuri'a a zaben gama gari a Zambiya cikin lumana

Mutane sun yi cincirindo a tashoshin zabe inda suka kada kuri'a a zaben shugaban kasa da ake kankankan tsakanin manyan 'yan takara biyu.

A kasar Zambiya an rufe rumfunan zabe bayan zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki da aka gudanar a wannan Alhamis. 'Yan kasar sun yi dogayen layuka a tashoshin zaben na gama gari, inda masu aiko da rahotanni suka ce komai ya tafi salin alim, duk da tashe-tashen hankulan da aka fuskanta lokacin yakin neman zabe. Sai dai jami'ai na fargabar barkewar wani tashin hankali bayan kawo karshen zaben, ko kuma bayan an sanar da sakamakon karshe a zaben inda ake kankankan tsakanin manyan 'yan takarar neman shugabancin kasar wato shugaba mai ci Edgar Lungu da abokin hamaiya kuma dan kasuwa Hakainde Hichilema. Shugaban tawagar sa ido ta kungiyar Tarayyar Afirka kuma tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ce ya yi murna da yadda abubuwa suka gudana kawo yanzu.