An kammala hare-hare a Saint Denis | Labarai | DW | 18.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kammala hare-hare a Saint Denis

Saint Denis daya daga cikin ungwannin da ke kewaye da Paris ne, kuma dakarun yaki da ta'addanci sun shafe sa'o'i bakwai suna ba ta kashi wadanda ake zargi 'yan ta'adda ne.

Dakarun yaki da ta'addanci sun kammala aiyukansu a yankin Saint Denis daya daga cikin yankunan da ke kewaye da birnin Paris na kasar Faransa, bayan da suka shafe sao'i bakwai, kamar yadda kakakin gwamnatin Faransa ya bayyana. A cewar rahotanni dai baki daya mutane bakwai ne aka kama a yanzu haka. Sai dai a yayin da Faransar ke kokarin farfadowa daga raunin da wadannan hare-hare suka yi mata, gwamnatin kasar na kokarin aiwatar da wasu sabbin matakai na yaki da ta'addanci wadanda ta gabatar cikin wani kudurin doka. Kakakin gwamnatin Stephane Le Foll ya sanar da wasu daga cikin abubuwan da ke cikin kudurin dokar

"Kudurin dokar ya shawarci da a kara wa'adin dokar ta bacin da aka sanya tun da daren 14 ga watan Nuwamba har na tsawon watanni uku kamar dai yadda aka yi a shekara ta 2005 duk da cewa yanayin biyu ba daya ba ne, kuma dokarta sake kwaskware wasu daga cikin dokokin da aka yi tun a watan Afrilun shekarar 1955 domin ta tabbatar da cewa komai ya tafi yadda ya kamata"