An kammala aikin share gubar darma a Najeriya. | Labarai | DW | 23.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kammala aikin share gubar darma a Najeriya.

Ƙungiyar Medecins Sans Frontieres wato MSF ta ce, ta fara yin aikin ba da magunguna ga wasu yara da suka kamu da cututuka,saboda shaƙar iskan gubar darma a jihar Zamfara da ke a yanki arewa maso gabashi na ƙasar.

Ƙungiyar ta MSF ta ce a shekarun 2010 yara kusan 400 suka mutu waɗanda suka shaƙi gubar a tsawon watanni shidda a lokacin da suke ƙoƙarin haƙo ma'adinai ta hanyar gargajiya a jihar Zamfara. Wani jami'in ƙungiyar ya shaida cewar ma'aikatan su na daf da kammala aikin share gubar da ta bazu a cikin ƙasa da ruwa na yanki.

Kuma garin Bagega da ke cikin jihar ta Zamfara nan ne, lamarin ya yi ƙamari. Tun farko dai an yi jinkiri wajan yin aikin saboda rashin samun taimakon ƙasashen duniya wanda a ƙarshe suka ware Euro miliyan biyu da rabi saboda aikin.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu