An kame wani dan kishin Islama dangane da kisan Rafik Hariri a Lebanon | Labarai | DW | 23.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kame wani dan kishin Islama dangane da kisan Rafik Hariri a Lebanon

A kasar Lebanon an kame wani musulmi mai tsattsauran ra´ayi, wanda aka zarga da hannu a kisan gillar da aka yiwa tsohon FM kasar Rafik Hariri. Kamar yadda kafofin yada labaru suka nunar mutumin da aka kamen dai dan wata kungiyar Musulmi ne dake da alaka da kasar Syria. An kame shi ne kuwa jim kadan bayan bayyana rahoton bincike na MDD a dangane da kisan da aka yiwa Hasriri. Rahoton wanda alkalin Jamus Detlev Mehlis ya rubuta ya zargi jami´an hukumomin leken asirin Syria da na Lebanon da hannu a fashewar bam din da yayi sanadiyar tsohon FM a ranar 14 ga watan fabrairu. Tuni dai Syria ta musanta wannan zargi tana mai cewa bai da tushe bare makama, kuma ya na da wata manufa ta siyasa.