An kame matan ′yan siyasar Nijar a badakalar fataucin jarirai | Labarai | DW | 25.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kame matan 'yan siyasar Nijar a badakalar fataucin jarirai

Hakan na zuwa ne bayan bankado wani gungun masu fataucin jarirai biyo bayan wani bincike na hadin guiwa tsakanin 'yan sandan Nijar, Najeriya da kuma Benin.

A Jamhuriyar Nijar an kame matan wasu fitattun 'yan siyasar kasar su biyu biyo bayan bankado aika-aikar wata kungiya da ke fataucin jarirai a wannan mako. Wata majiyar 'yan sanda ta fada wa kamfanin dillancin labarun AFP a wannan Larabar cewa tun a ranar Litinin aka cafke mutane fiye da 20 a wani bincike da jami'an sandan kasashen Najeriya, Benin da kuma Nijar din ke yi na wadanda ake zargi da hannu a fataucin jariran. Yawancin wadanda aka kamen dai mata ne da suka hada da matan tsohon Firaministan Nijar kuma kakakin majalisar dokoki a yanzu Hama Amadou, mutumin da ake wa kallon zai zama babban mai kalubalantar shugaba Mahamadou Issoufou a zaben shekarar 2016. An kuma tsare matar ministan aikin gona Abdou Labo. Ana zargin cewa an shiga da yaran Nijar ne daga Najeriya bayan an bi da su ta Benin. Jami'an kiwon lafiya na daga cikin wadanda ke hannun 'yan sanda.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe