An kame masu satar yara a Cote d′Ivoire | Labarai | DW | 02.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kame masu satar yara a Cote d'Ivoire

Hukumomin tsaro sun kame mutane kusan guda dubu waɗanda ake zargi da hannu wajen sace yara ƙanana.

Da yake magana da manema labarai ministan tsaro na ƙasar Paul Koffi Koffi ya ce yawancin waɗanda aka cafke,an kame su ne a kusa da makarantu da kuma cibiyoyin intanet waɗanda kawo yanzu aka rufe cibiyoyin sama da 500 waɗanda ba su da izinin yin aikin.

Sannan kuma ya ce daga cikin waɗanda ake tsare da su bayan bincike za a saki waɗanda ba su da laifi.Tun watannin ukun da suka wucce 'yan sanda a ƙasar ke ƙoƙarin murƙushe yunƙurin sace-sacen yaran wanda ke ƙarewa da kisan kai.