An kame ma′aikatan jirgin ruwan Girka a Kamaru | Labarai | DW | 31.12.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kame ma'aikatan jirgin ruwan Girka a Kamaru

A kasar Kamaru wasu mutane dauke da makamai sun kai farmaki kan wani jirgin ruwan kasar Girka inda suka yi awon gaba da takwas daga cikin ma'aikatan jirgin.

Wasu mutane dauke da makamai sun kai hari tun da sanhin safiyar wannan Talata kan wani jirgin ruwan dakon mai na kasar Girka a tashar ruwan birnin Limbe na aksar Kamarou inda suka yi awon gaba da ma'aikatan jirgi guda takwas da suka hada da Girkawa biyar da 'yan kasar Philippin biyu da dan Ukraine daya.

 Ministan sufurin ruwa na kasar Girka ne ya sanar da hakan a cikin wani sanarwa da ya fitar inda ya ce daya daga cikin ma'aikatan jirgin ruwan su 28 ya jikkata a kafa a sakamakon harbin bindiga.

 Hare-hare kan jiragen ruwa da garkuwa da mutane domin neman kudin fansa abu ne da ya zamo ruwan dare a mashigin ruwan Guinea da ake dauka a matsayin yanki mafi hadarin fashin teku a duniya.