An kama ′yan kungiyar ′yan uwa Musulmi 516 | Labarai | DW | 26.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kama 'yan kungiyar 'yan uwa Musulmi 516

Rundunar 'yan sanda Masar ta kame 'yan kungiyar 'Yan Uwa Musulmi 512 biyo bayan tashin hankalin ya barke yayin bikin tunawa da ranar da guguwar neman sauyi.

Ministan ma'aikatar cikin gidan Masar din Mohamed Ibrahim ya shaidawa manema labarai a birnin alkahira cewar an kama mutanen ne da laifin yin harbe-harbe da kuma dasa ababan fashewa baya ga lalata wasu wurare da suka yi sanadiyyar fashewar bam din da suka sanya.

To sai dai a daura da wannan, kungiyoyi na kare hakkin bani Adama daga ciki da wajen kasar na cigaba da sukar lamirin gwamnati na amfani da karfin da ya wuce kima wajen tarwatsa masu zanga-zanga, inda suka bukaci da a gudanar da bincike kan rikicin na jiya da ya yi sanadin rasuwar mutane sama da 20.