An kama wasu masu alaka da harin Dortmund | Labarai | DW | 12.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kama wasu masu alaka da harin Dortmund

'Yan sanda sun kama wasu mutane guda biyu wadanda ake zargi da hannu a harin bam da aka kai a kan motar kungiyar 'yan wasan kwallon kafa na Dortmund.

Wasu majiyoyi na 'yan jarida sun ce mutanen biyu sun hada da wani dan kasar Iraki dan shekaru 25 da ke a Wuppertal da kuma wani dan Jamus dan shekaru 28 da ke a Fröndenberg dukkaninsu masu kishin addini.Tuni dai da 'yan sandar suka kaddamar da bincike a gidajen mutanen, wadanda ake kyautata zaton cewar sunna da alaka da harin.Ko da shi ke ma 'yan sandar sun ce suna ci gaba da yin bincike domin tantance gaskiyyar lamarin.