An kama wasu da ake zargi da hannu a kisan wani Janar a Burundi | Labarai | DW | 10.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kama wasu da ake zargi da hannu a kisan wani Janar a Burundi

A makon da ya gabata wasu suka Kai hari kan Janar Adolphe Nshimirimana a Bujumbura babban birnin kasar Burjndi, inda suka hallaka shi.

Ofishin ministan shari'ar kasar Burundi ya sanar cewa, an gano wadanda suka aikata kisan gilla ga Janar Adolphe Nshimirimana da ke a matsayin na hannun damar shugaban kasar Pierre Nkurunziza.

Ta shafinsa na sadarwa na zumunta ne dai babban alkalin kasar ta Burundi, ya sanar da wannan labari, inda kuma ya ce suna ci gaba da neman sauran mutanen da ma wadanda suka kitsa kisan gillan domin su gurfana a gaban kuliya.

Kakakin 'yan sandan kasar Pierre Nkurikiye ya tabbatar da wannan sanarwa ta babban alkalin kasar amma kuma kawo yanzu ba a ambaci wani suna daga cikin wadanda aka ce an kaman ba.

A yammacin ranar Lahadi ma dai an yi ta jin karan harbe-harbe a Bujumbura babban birnin kasar ta Burundi.