An kama wani ɗan Ƙungiyar IS a Moroko | Labarai | DW | 18.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kama wani ɗan Ƙungiyar IS a Moroko

Hukumomin tsaro a Moroko sun ba da sanarwar cewar sun cafke wani ɗan ƙasar Beljiam wanda ke da hannu a hare-haren Faransa.

Mutumin wanda aka kama a garin Al Mohammadiya kusa a gidan mahaifiyrasa .
Bincike jami'an tsaro ya nuna cewar ya je Siriya tare da ɗaya daga cikin 'yan ƙunar baƙin waken na Paris inda ya samu horo daga Ƙungiyar Al-Nosra kafin daga baya ya shiga Ƙungiyar IS. Hukumomin tsaron na Moroko sun daɗe suna gudanar da bincike a kan mutumin wanda yake yawan zuwa ƙasar kai a kai.Mutane kusan 130 suka mutu a hare-haren na Paris waɗanda aka kai a ckin watan Nuwamba da ya gabata