An kama wani ƙusa na Boko Haram | Labarai | DW | 15.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kama wani ƙusa na Boko Haram

Hukumar 'yan sanda a Najeriya ta ce ta cafke wani jigo na Ƙungiyar Boko Haram wanda a ke yi wa laƙabi da sunan sarkin yanka.

Mohammed Zakari mai kimanin shekaru 30 da haifuwa, an kama shi ne a wani farmaki da jami'an tsaro suka kai a kan hanyar garin Darazo da ke cikin jihar Bauchi da ke a yankin arewacin ƙasar.

Kakakin 'yan sandar na Najeriya Frank Mba,ya ce Zakari yana da hannu dumu-dumu a cikin kisa na yara ƙanana da mata a hare-haren da Ƙungiyar ta Boko Haram ta kai a yankuna da dama na arewacin ƙasar. Wannan kamu dai na zuwa ne a sa'ilin da ake ci gaba da samun ƙaruwar kai hare-haren na masu kishin addini a Najeriya.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Suleiman Babayo