An kama wani ƙusa na ƙungiyar Al-Qaida | Labarai | DW | 08.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kama wani ƙusa na ƙungiyar Al-Qaida

Za a gurfanar da Sulaiman Abu Ghaith wanda siriki ne, kana kuma na hannun dama ga marigayi Osama bin Laden a gaban kotu.

Ana tuhumar Abou Ghaith ɗin ne da laifin kai hari a cikin watan Satumba na shekara ta 2001 a Amurkan wanda a ciki kusan mutane dubu ukku suka mutu.

Mataimakiyar ministan tsaro na Amurka Lisa Monaco ta ce kamun na ɗan ta'addar na da cike da mahimmanci a kokowar da suke yi ta yaƙi da ta'addanci a duniya. Ko da shi ke hukumomin Amurka basu bayyana yadda aka kamashi ba. Amma wata jaridar a ƙasar Turkiya ta ce an kama shi ne a ƙarshen watan Janeru a birnin Ankara, kana aka tusa ƙeyarsa zuwa ƙasar Jordan kafin da ga can a kai shi Amurka.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar.