An kama karin mutane 150 a Tunisiya | Labarai | DW | 12.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kama karin mutane 150 a Tunisiya

Mahukuntan kasar Tunisiya sun kame wasu mutane 150 da suka hada da jagoran 'yan adawa sakamakon zanga-zangar nuna bacin rai dangane da tsadar kayayyakin matsarufi.

Adadin wadanda ke hannun jami'an tsaro ya kai  mutane 800 sakamakon wata zanga zanga da 'yan kasar suke gudanar a wannan makon saboda hawan farashi da kuma karin kudin haraji.

Zanga zangar ta dada daukar zafi ne a ranar Litinin yayin da aka kashe wani daga cikin masu zanga zangar, abin da yayi sanadiyyar kone-konen kayayyakin gwamnati, wanda hakan yasa mahukuntan kasar suka raba sojoji cikin manyan biranen kasar.

Masu rajin kare hakkin dan Adam da kuma 'yan adawa na kira da a ci gaba da wannan zanga-zanga a Tunis babban birnin kasar tun daga Jumma'a zuwa ranar Lahadi, kuma ranar da zata kasance ranar bikin tunawa da hambarar da mulkin shugaba Zine El-Abidine Ben Ali.

A halin yanzu dai an fara samun kwanciyar hankali a kasar koda yake a daren Alhamis zuwa Jumma'a  jami'an tsaro sun cafke mutane 150 wadanda da ke da hannu a rikicin daya tayar da hankalin al'ummar kasar ta Tunisiya.