1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masar ta kama dan kungiyar Muslim Brotherhood

August 28, 2020

Hukumomi a Masar sun kama wani jigo a kungiyar 'yan uwa Musulmi ta Muslim Brotherhood Mahmoud Ezzat a birnin Alkahira.

https://p.dw.com/p/3hdxH
Mahmoud Ezzat
Hoto: picture-alliance/dpa

Gwamantin kasar ta Masar ta zargi Mahmoud Ezzat da shiga cikin harkar ta'addanci tare da karbar wasu kudade da ba su dace ba. Mahukuntan sun ce tun a shekara ta 2013 Ezzat ke aikata manyan laifuka da suka hada da jagorantar kisan gilla da ma dana bama-bamai a Masar. 

A baya dai an taba yanke wa Ezzat din hukuncin kisa bisa wasu laifuka da hukumomin na Masar suka ce ya aikata. Sai dai kuma dan kungiyar ta Muslim Brotherhood, ya sha musanta duk zarge-zargen.