An kama bakin haure a Italia | Labarai | DW | 21.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kama bakin haure a Italia

Italy/Immgrant

Jamian kwastan na kasar Italia sun kame bakin haure samada dari shida a ,wadansu kananan jiragen ruwa hudu.

Jamian sunce jirgin farko wanda yake dauke da mutane 177 sun ganoshine a tsibirin Lampedusa da yake tsakanin tsibirin cicily na kasar Italian da kuma gabar ruwan kasar Libiya.

Bayan cafke jirgin na farkone daga bisani kuma suka sake kama wadansu jiragen na ruwa dauke da bakin hauren kusan 480.

Rukunin farko na bakin su 177 an kai su wani sansanin matafiya da ke kusa da filin jirgin tsibirin da aka kamasu.

Mai magana da yawun jamian kanar Marcello Marozcca yace bisa ga dukkan alamu jiragen sun fitone daga Africa ta arewa musamman ma kasar Libya.

Tun farkon wannan shekarar dai Italiyan ta tsare bakin haure fiye da 15000 wadanda suke kokarin shiga kasar ba da izini ba ta gabar kudancin tekun kasar inji maaikatar cikin gida ta kasar.