An kai wani sabon hari a Turkiya | Labarai | DW | 07.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kai wani sabon hari a Turkiya

Wani abu ya fashe a birnin Santanbul na Turkiya, inda ake tsammanin an kai hari ne a kan jami'an tsaro.

Rahotanni daga birnin Santanbul na Turkiya na nuni da cewa an samu wata fashewa a tsakiyar birnin kusa da wajen shiga motocin safa. Wasu kafofin yada labarai sun ruwaito cewa akwai wasu mutane da suka samu raunika kuma tuni aka tura motocin daukar marasa lafiya domin kai su asibiti a basu kulawar gaggawa, sakamakon faruwar lamarin na safiyar wannan Talata. An kai harin ne a kan motar jami'an 'yan sanda.