An kai wani sabon hari a Bama | Labarai | DW | 04.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kai wani sabon hari a Bama

Hare-haren 'yan bindiga na ƙara halaka rayukan al'umma a jihar Borno, inda a ƙasa da kwana uku aka kai hari sau biyu kuma aka hallaka kimanin mutane 60.

Rahotanni daga Maiduguri babban birnin jihar Borno sun bayyana cewa, wasu mutane da ake kyautata za ton 'yan ƙungiyar Boko Haram ne, sun kai wani sabon farmaki a wani ƙauya kusa da Bama, inda suka hallaka mutane kimanin 30, yayinda suka jikka wasu dadama, kana suka kone gidaje sama 300. Wani jami'in ƙaramarhukumar Bama yace, maharan kimanin 70 dauke makamai, a kan babru 15, da motocin akori-kura, sun dira a ƙauyenne ba zato. Matsalar katse sadarwa a jihar Borno ta ƙara dagula al'amura, inda ƙauyawa basu da wata hanya ta sanarda halinda suke ciki koda wane kisan gilla da ake yi musu. Domin kuwa gwamnati ta katse sadarwa tun lokacin aka ƙaddamar da dokar ta-ɓaci. Jimi'in da ya bada labarin, yace harin da akai, ya zo ne bayan da a ƙarshen mako wasu 'yan bindi su ka yi wa wasu mutane dake dawowa daga daurin aure kwantan ɓauna, inda nan ma suka kashe 30 cikin harda ango. Maharan dai sun kashe dabbobi, kana suka lalata shaguna tare da yin sata ta kimanin Naira miliyan hudu.

Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Saleh Umar Saleh