An kai sabon hari a garin Baquba dake Iraq | Labarai | DW | 27.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kai sabon hari a garin Baquba dake Iraq

Wasu bama bamai a garin baquba na Iraqi sunyi sanadiyyar rasuwar mutane 8 , bakwai daga cikin su duk yan gida daya.

A cewar jami´an yan sandan bama baman sun tashi da mutane bakwan ne a yayin da suke kwance a lambun harabar gidan su, a sabili da zafi sakamakon yawan dauke wutar lantarki.

Ya zuwa yanzu dai babu masaniyar ko da man can anyi niyyar kai wannan harin ne ga wadannnan mutane ko kuma kaddara ce ta hau su.

Garin dai na Baquba na daga cikin manya manyan birane a Iraqi da ake fuskantar yawaitar tashe tashen bama bamai da kuma hare haren yan kunar bakin wake.

Har kawo yanzu dai babu wani mutum ko kungiya da tayi ikirarin hannu a cikin kai wannan hari.

Jami´an Amurka dai sun yi gargadin cewa da alama ire iren wadannan hare hare ka iya karuwa, a cikin wannan wata na azumi.