An kai mummunan hari cocin Koptik a Masar | Labarai | DW | 09.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kai mummunan hari cocin Koptik a Masar

Tagwayen hare haren wadanda aka kai Cocin mabiya darikar Koptik ya hallaka mutane akalla 40 tare da jikata wasu da dama.

A kasar Masar wasu tagwayen hare-haren ta'addanci da aka kai a wasu Coci-Coci a birane biyu na kasar a wannan Lahadi sun yi sanadiyyar mutuwar mutane kimanin 40. Gwamnatin kasar ta tabbatar da cewa hari na farko an kai shi ne da misalin karfe goma na safiyar yau a Cocin Kiristoci mabiya darika Koptika na garin Tanta da ke a nisan kilomita 120 arewacin birnin Alkahira inda mutane akalla 25 suka rasu a yayin da wasu 78 suka ji rauni 

Tashar talabijin ta Etra News mai zaman kanta a kasar ta Masar ta nuna cikin ginin Cocin da irin yadda jini ya fantsama ko ina a saman ginin dama yadda kujerun zama na cikin cocin suka kaca kaca

Hari na biyu wanda na kunar bakin wake ne an kai shi ne a Cocin birnin Alexandrie, inda ya zuwa yanzu aka tabbatar da mutuwar mutane 11 a yayin da wasu 35 suka sami raunuka. Tuni dai Kungiyar IS ta dauki alhakin kai wadannan hare-hare na wannan rana ta lahadi a kasar ta Masar.