An kai harin ta′addanci a Barcelona | Labarai | DW | 17.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kai harin ta'addanci a Barcelona

A birnin Barcelona na kasar Spain, bayanai na cewa ana fargabar asarar rayuka lokacin da wata motar dakon kaya ta kutsa cikin cunkoson jama'a a yankin Larambla da yawon shakatawa.

Rahotannin da ke fitowa birnin Barcelona na kasar Spain, na cewa an sami asarar rayuka lokacin da wata motar dakon kaya ta kutsa cikin cunkoson jama'a a yankin La Ramblas na masu yawon shakatawa ke ziyarta.

Da fari dai kafofin labaran kasar sun ce kimanin mutane 13 ne ake fargabar suka halaka tare da jikkatar wasu kimanin 50, a harin da jami'an 'yan sanda suka ce na ta'addanci ne. 

Tuni hukumomi suka killace inda aka kai harin, tare da kira ga jama'a da su kauracewa yankin. Shaidu sun ce sun ga wasu mutane da ake zargi da hannu a harin, sun rufe kansu cikin wani shagon sayar da abinci.