An kai harin bam a Gombe daf da yaƙin neman zaɓe na PDP | Labarai | DW | 02.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kai harin bam a Gombe daf da yaƙin neman zaɓe na PDP

Mutane aƙalla guda uku suka mutu yayin da wasu 18 suka jikkata.

An ba da rahoton cewar wani bam ya fashe a cikin wani wurin ajiye motoci da ke kusa da filin ƙwallon ƙafa na garin Gombe da ke a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Masu aiko da rahotannin sun ce bam ɗin ya fashe,mintocin uku bayan da ayarin motocin shugaban ƙasar Goodluck Jonathan ya ficce daga wani gangamin yaƙin neman zaɓe a filin ƙwallon wanda jam'iyyarsa da ke yin mulki wato PDP ta shirya.