1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kai hari yammacin Nijar

April 18, 2021

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na cewa akalla fararen hula tara ne suka rasa rayukansu a wani harin da 'yan bindiga suka kai a kauyen Gaigorou a yankin Tillaberi.

https://p.dw.com/p/3sCQF
Symbolild Niger Islamistischer Terrorismus
Hoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

Rahotannin sun baiyana cewa mahara sun farwa mutane ne a makabarta yayin da daga bisani suka bude wuta ga wasu mazauna kauyen.

A baya-bayan nan dai mahara sun zafafa kai hare-hare yankin Tillaberi da ya hada iyakokin kasashen Nijar din da Mali da kuma Burkina Faso. Tun daga farkon wannan shekarar akalla mutane dari 3 ne suka rasa rayukansu a wasu hare-hare 3 da aka kai yankin, sai dai har kawo yanzu babu wata kungiya da ta fito ta dauki alhakin kai hare-haren.