An kai hari ofishin jakadancin Tunisiya da ke kasar Libiya | Labarai | DW | 12.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kai hari ofishin jakadancin Tunisiya da ke kasar Libiya

An yi garkuwa da ma'aikata 10 na ofishin jakadancin Tunisiya da ke kasar Libiya lokacin da wasu tsageru dauke da makamai suka kutsa ofishin

Wasu tsageru dauke da makamai sun kutsa ofishin jakadanci kasar Tuniya da ke kasar Libiya tare da garkuwa da ma'aikata 10.

Mai-magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Tunisiya ya ce babu bayani kan maharan, da kuma yadda aka yi garkuwa da mutanen. Kasar ta Libiya da ke yankin arewacin Afirka ta fada rudacin siyasa da tattalin arziki tun bayan juyin-juya halin shekara ta 2011, wanda ya kawo karshen gwamnatin Marigayi Ma'ammar Gaddafi ta fiye da shekaru 40.

A wani labarin mahukuntan kasar Romaniya sun kori 'yan kasar Tunisiya biyu daga kasar saboda suna da nasaba da kungiyar 'yan ta'adda ta IS mai neman kafa daular Islama a kasashen Iraki da Siriya.