An kai hari kan ofishin MDD a Mali | Labarai | DW | 14.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kai hari kan ofishin MDD a Mali

Jami'an Majalisar Dinkin Duniya a Mali, sun ce wasu 'yan bindiga dauke da manyan makamai sun far wa ofishinsu a yankin arewacin kasar.

Wasu 'yan bindiga sun kai hari kan wani ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke arewacin birnin Timbuktun kasar Mali. Jami'an Majalisar ta Dinkin Duniya da ke Malin, sun ce 'yan bindigan wadanda ba a kaiga tabbatar da inda suka fito ba, sun far wa ofishin na su ne dauke da manyan bindigogi masu sarrafa kansu.

Mai magana da yawun ma'aikatar, Radhia Achouri, ta shaida wa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa maharan na ta buda wuta ne babu kakkautawa. Wasu bayanan na cewa tuni aka aike da dakarun kwantar da tarzoma don ganin yadda za a murkushe harin. Tuni ma dai Majalisar Dinkin Duniyar ta yi tir da faruwar wannan al'amari.