An kai hari kan jirgin ruwan Iran | Labarai | DW | 07.04.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kai hari kan jirgin ruwan Iran

Ma'aikatar harkokin wajen Iran ta tabbatar da lalata wani jirgin kasarta a Bahar Maliya a wasu hare-haren makamai masu linzami da aka kai.

An dai ga jirgin dakon kaya mai suna Savis a tekun da ke kusa da Yemen tun shekara ta 2016 wanda ke jefa shakkun cewar ana amfani da shi ne a matsayin sansanin ‘yan tawayen Huthi da ke samun goyon bayan Iran.

Kakakin ma'aikatar, Said Khatibzadeh ya ce babu wanda ya rasa ransa a harin da aka kai wa jirgin. An dai zargi Yemen da kai harin, sai dai har kawo yanzu Yemen din bata ce komai ba.