An kai hari kan jami′an tsaro a Burundi | Labarai | DW | 27.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kai hari kan jami'an tsaro a Burundi

Mutane akalla uku sun halaka a cikin wani hari da wasu 'yan bindiga suka kai da gurneti kan jami'an tsaro a birnin Bujumbura na kasar Burundi

A Burundi akalla mutane uku sun mutu a yayin da wasu kimanin 15 suka ji rauni daga jiya zuwa yau Talata a cikin wani artabu da ya hada jami'an tsaron kasar da wasu 'yan bindiga a birnin Bujumbura.

Kakakin hukumar 'yan sanda ta birnin na Bujumbura ya wallafa a saman shafinsa na tweeter cewa a yammacin jiya Litanin wani soji ya hallaka wani mai tabin hankali da ya kai mai hari da mashi a unguwar Chobitoke da ke Arewa maso Yammacin birnin. Hari na biyu wasu da ya kira 'yan ta'adda ne suka kai shi da gurneti da kuma bindiga kan rukunin wasu 'yan sanda da sojoji a dai wannan unguwa ta Chibitoke

Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ruwaito cewa an share sama da awa daya ana jin karan pashewar gurneti da aman rokoki da wasu manyan bindigogi a cikin birnin. An dai kiyasta cewa gurneti akalla 25 ne aka hari jami'an tsaro da su a wannan Talata a birnin na Bujumbura inda maharan suka yi ikrarin kashe 'yan sanda akalla 20.