1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kai hari kan dalibai a Japan

May 28, 2019

Wani mutum dauke da wukake ya afka wa wasu kananan yara, inda ya aikata kisa tare da jikkata sama da mutum 10 a wajen birnin Tokyo.

https://p.dw.com/p/3JGaT
Japan Messerangriff in Kawasaki
Hoto: Reuters/Kyodo

Hukumomi a Japan, sun tababatar mutuwar akalla mutum uku yayin da wasu 16 da suka hada da yara 'yan makarantar fimarare suka ji rauni a harin.

Lamarin da ya faru a yankin Kawasaki kusa da birnin Tokyo, ya rutsa ne da 'yan matan da tsakanin shekaru shida zuwa bakwai ba, a lokacin da suke jiran motar bas da za ta kai su wata makaranta.

Akwai ma daya daga cikin 'yan matan da ta rasa ranta a cewar rahotanni a safiyar Talata.

'Yan sanda sun ce wani mutum da suke tsare da shi ma, ya mutu sakamakon daba wa kansa wuka da ya yi a wuya.

Hukumomi sun ce ba kai ga tabbatar da dalilin maharin na aikata wannan aikin ba, sai dai an ji shi yana ihun cewa ''sai na kashe ku''.

Japan dai na daga cikin kasashen da ke manan lafiya a duniya.