An kai hari fadar gwamnatin Afghanistan | Labarai | DW | 25.06.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kai hari fadar gwamnatin Afghanistan

Wasu 'yan kunar bakin wake a Afghanistan sun tada bam a fadar shugaban kasar da ke kabul kafin daga bisani 'yan bindiga su shiga dauki ba dadi da jami'an da ke tsaron fadar.

Harin dai ya faru ne a yankin da ake ganin ya fi ko ina tsaro a kasar wanda ya kunshi shelkwatar tsaro ta NATO da ofishin jakadancin Amurka da kuma ma'aikatar tsaron kasar.

Wannan tashin-tashina dai ta wakana ne da sanyin safiyar wannan Talatar gabannin wani taron manema labarai da shugaban kasar Hamid Karzai zai jagoranta. Sojin gwamnatin kasar dai sun ce sun hallaka maharan baki dayansu kuma babu wani soja ko fara hula da ya rasa ransa a harin.

Tuni dai kungiyar nan ta Taliban ta dauki alhakin wannan harin a wani sakon imel da kakakin kungiyar Zabihullah Mujahid ya aikewa manema labarai. Wannan dai na zuwa ne kwanaki kalilan bayan da kungiyar ta Taliban ta ce ta amince da ta shiga wani zama na sasantawa da mahukuntan kasar.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Saleh Umar Saleh