An kai hari da gurneti a kotun kolin Banizuwela | Labarai | DW | 28.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kai hari da gurneti a kotun kolin Banizuwela

Wani jirgi mai saukar angula na hukumar 'yan sanda a Banizuwela ya kai hari a kotun koli da kuma a ma'aikatar ministan cikin gida

Shugaba Maduro na Banizuwela da gwamnatinsa sun yi tir da Allah wadai da abin da suka kira harin ta'addanci bayan da wani jirgin mai saukar angulu na hukumar 'yan sandar kasar ya harba wasu gurneti- gurneti a cikin ofishin kotun kolin kasar da ke a birnin Caracas kana ya buda wuta a kan ma'aikatar ministan cikin gida ta kasar. 

Sai dai shugaban ya sanar da bai wa dukkanin rindunonin sojojin kasar umarnin fitowa domin tabbatar da tsaro, inda yanzu haka aka girke sojoji da tankokin yaki a kewayen fadar shugaban kasar. Shugaba Maduro ya ce nan ba da jimawa ba za su kame jirgin da ma wadanda suka kai wadannan hare-hare na ta'addanci, sai dai bai yi bayani ba ko an samu mutuwa ko lalacewar wasu abubuwa a sakamakon harre-haren da aka kai. 

Tun a ranar daya ga watan Aprilun wannan shekara ne dai Shugaba Maduro ke fuskantar tarzomar al'umma wadanda ke neman ganin ya yi murabus inda kawo yanzu mutane 76 suka rasu a cikin watanni uku daga cikin masu zanga-zangar kyamar gwamnatin tasa.