1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kai hari mai muni a wani barikin sojin Nijar

May 19, 2020

An kai hari a kan wani barikin sojin Jamhuriyar Nijar a yankin Diffa, inda ake zullumin an samu asarar rayukan sojoji. Ba wanda ya dauki alhakkin wannan hari, amma ya yi kama da wanda Boko Haram ke kaiwa.

https://p.dw.com/p/3cUL1
Niger Agadez Wrack eines Selbstmordattentats
Hoto: AFP/B. Hama


Shaidun gani da ido irin su Mara Mamadou dan kungiyar farar hula sun ce harin ya faru ne ranar Litinin da misalin karfe 11 na dare, yana mai cewa maharen sun lalata wasu gine-gine, an kuma samu asarar rayuka. Wani dan siyasa a yankin na Diffa ya ce harin ya yi kama da na 'yan Boko Haram, duk da cewa kungiyar ba ta dauki alhakin harin ba.

Kawo yanzu babu adadin mutanen da suka mutu a harin na barikin sojojin Blabrine. A baya ma dai an taba kai wa wannan barikin soji hari, inda watan Oktoban da ya gabata irin wannan harin ya kashe sojojin Nijar guda 12.