1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya: An kai hari a ofishin jakadancin Amirka

August 20, 2018

'Yan bindiga sun buda wuta kan ofishin jakadancin Amirka da ke a kasar Turkiyya, kamar yadda jami'ai suka tabbatar.

https://p.dw.com/p/33Q8w
Türkei - Schüsse in US Botschaft in Ankara
Hoto: picture-alliance/abaca/Depo Photos

Rahotanni daga kasar Turkiyya na cewa wasu dauke da bindigogi sun buda wuta kan ofishin jakadancin Amirka da ke a kasar, sai dai babu labarin wani da halaka a lamarin.

A cewar jami'an jakadancin Amirka a Turkiyyar da ma wasu na gwamnatin kasar, da jijjifin safiyar wannan Litinin 'yan bindigar suka harba harsasai sau shida daga cikin wata motar da ke wucewa ta ofishin wanda ke Ankara babban birnin kasar.

Kakakin gwamnatin Shugaba Racep Tayyip Erdogan, Ibrahim Kalin, ya bayyana hakan da cewa wani yunkuri ne na ta'azzara lamura tsakanin Turkiyya da Amirka, da a yanzu ke takaddamar cinikayya da ta diflomasiyya.

Ofishin jakandancin na Amirka wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce babu wani da ya mutu ko ya ji rauni, tare kuma da yaba wa jami'an 'yan sandan Turkiyyar da irin binciken da suke gudanarwa a kan harin.