An kai hari a masallacin Landan | Labarai | DW | 20.02.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kai hari a masallacin Landan

Jami'an tsaro a Landan, sun tabbatar da kama wani da ya afka wa musulmi da wuka da ke tsakiyar birnin. Hakan ya faru ne bayan aukuwar hare-haren kyamar baki a Jamus.

'Yan sanda a Birtaniya, sun ce sun kama mutumin da ya kai hari da wukar inda ya jikkata ladanin masallacin da ke tsakiyar birnin Landan.

'Yan sandan sun ce tuni aka kai ladanin asibiti, inda ake dakon sakamakon likitoci.

Wasu hotunan da wasu masallata suka yada a shafin twitter, sun nuno 'yan sandan damke da mutumin da ake zargi da kai harin.

Hakan kuwa na faruwa ne bayan wani hari da wani ya kai kan wasu baki a wajen birnin Frankfurt da ke nan Jamus cikin daren da ya gabata, inda ya kashe rayuka mutum akalla tara a wasu wuraren shan tabar shisha.