1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

An kai hari a masallaci a Afghanistan

October 15, 2021

Mutane da dama ne ake fargabar sun salwanta a Afghanistan sakamakon hari da aka kai a kan masallata a wannan Juma'ar. Haka zalika lamarin ya jikkata da dama.

https://p.dw.com/p/41jqs
Afghanistan Bombenanschlag auf schiitische Moschee in der afghanischen Provinz Kandahar
Hoto: Murteza Khaliqi/AA/picture alliance

Akalla mutane 35 ne suka mutu yayin da wasu da wasu gommai suka jikkata a wani sabon harin bom da aka kai a kan masallata a kudancin kasar Afghanistan.

Gwamnatin Taliban da ke jagorantar al'amura a Afghanistan din da ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce an kai harin ne a masallacin Juma'a na 'yan Shi'a da ke a lardin Kandahar.

Gwamnatin lardin ta ce tana bincike kan harin na nakiya mai kama da na makon jiya da aka kai a kan Musulmi lokacin sallar Juma'a a lardin Kunduz da ke arewacin kasar.

Kasar ta Afghanistan karkashin sabuwar gwamnatin Taliban dai na fama da turjiya daga mayakan ISIS-K, wadanda ke tsananta hare-hare a yanzu bayan karbe iko daga gwamnatin dimukuradiyya a tsakiyar watan Agustan bana.