An kai hari a kan fararan hula a Ukraine | Labarai | DW | 19.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kai hari a kan fararan hula a Ukraine

Farar hula da dama suka mutu bayan wata roka ta faɗa kan jerin gwanon motocinsu a gabashin ƙasar ta Ukrain

Ana ci gaba da zargin juna tsakanin gwamnatin Ukraine da 'yan aware, kan wani harin da aka kai wa ayarin wasu motocin farar hula, da ke tserewa yaƙin da ake yi a gabshin ƙasar, inda mutane da dama suka rasu.

Yanzu haka Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce mutane dubu 340 suka tserewa tashin hankalin, yayin da gwamnati da 'yan aware ke gwabza faɗa. Rohotanni daga ƙasar ta Ukraine, sun bayyana cewar aƙalla gawarwarkin mutane 15 aka zaƙulo cikin ayarin motocin, wanda aka kai wa farmaki da wata rokar da aka haraba musu.

Mawallafi : Usman Shehu Usman
Edita : Abdourahamane Hassane