An kai hari a Jihar Adamawa-Najeriya | NRS-Import | DW | 19.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

NRS-Import

An kai hari a Jihar Adamawa-Najeriya

Mutane aƙalla guda tara suka mutu kana wasu da dama suka jikkata a harin da aka kai a cikin wata kasuwa a Garkiɗa.

Masu aiko da rahotannin sun ce mutumin da ya kai harin cikin kasuwar sayar da shanu ta garin na Garkiɗa.Tun farko jami'an tsaro sun gano yana ɗauke da bam, kuma a lokacin da suka bi shi da gudu ya sheƙa cikin kasuwar ya tayar da bam ɗin.

Wakilin DW a Yola ya ce yanzu haka hukumomin jihar na ƙoƙarin tantance,addadin mutane da lamarin ya rutsa da su.