An kai hari a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya | Labarai | DW | 29.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kai hari a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

An ba da rahoton cewar an kashe mutane aƙalla guda 15 mabiya addinin Kirista,da fada ɗaya, kana wasu mutane guda 30 suka jikkata.

Lamarin ya auku a sakamakon wani hari na ramuwar gayya da wasu mutane ɗauke da makamai suka kai a kan wata Coci da ke a Bangui babban birnin jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Cocin wacce ake kira da sunan ''Notre dame de Fatima'' na tsakiyar birnin kusa da unguwar musulmi. Masu aiko da rahotannin sun ce an gwabza faɗa tsakanin sojin sa kai Kirista 'yan Ƙungiyar Antibalka da musulmi a Cocin inda dubban jama'a suka samu mafuka.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru aliyu