An kai hare-haren ta′addanci a Mali | Labarai | DW | 28.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kai hare-haren ta'addanci a Mali

Rahotannin daga Mali na cewar wasu 'yan bindiga su kai harin rokoki a cibiyar rundunar kiyaye zaman lafiyata ta Majalisar Ɗinkin Duniya watau MINUSMA da ke a garin Kidal a yankin arewacin ƙasar.

Wani babban jami'in rundunar ya tabbatar da cewar 'yan bindiga sun kai hare-haren da sahin safiyar wannan Asabar inda suka kashe sojoji biyu da farar hula ɗaya kana wasu mutane 20 suka samu raunika. Wannan hari, na zuwa ne kwanaki kadan bayan harin da kungiyar alqaida reshen magreb AQMI, ta kai a makon jiya a cikin Otel Radisson da ke birnin Bamako wanda a cikin kusan mutane 20 suka rasa rayukansu