An kai hare-hare babban birnin Burkina Faso | Labarai | DW | 02.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kai hare-hare babban birnin Burkina Faso

Wasu mahara sun afka ofishin jakadanci da cibiyar raya al'adun kasar Faransa da kuma helkwatar rundunar sojojin Burkina Faso da ke babban birnin kasar Ouagadougou.

Masu aiko da rahotanni sun ce an ji karar harbe-harbe a wurin da lamarin ya faru sai dai daga bisani hukumomi sun bayyana cewar tuni an hallaka mutune hudu daga cikin mutanen da suka kai wannan hari.

Jama'ar da suke gurin sun bayyana cewar mutanen sun fito ne daga cikin wata mota tare da bude wuta kan mutane daga nan kuma suka nufi ofishin jakadancin Faransa.Tuni dai ofishin jakadancin ya aikewa ma'aikatnsa da wani sako ta shafin Facebook cewar kowa ya zauna a gida.

Kasar Burkina Faso na daga cikin kasashen yankin Sahara da suke fama da yaki da kungiyoyin ta'adda,wadanda suka yi sanadiyyar rasa rayuka da raba dubban jama'a da muhallan su tare da kassara tattalin arzikin kasar.