An kafa gwamnatin rikon kwarya a Libiya | BATUTUWA | DW | 05.02.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

An kafa gwamnatin rikon kwarya a Libiya

Bangarorin da basa ga maciji da juna na Libiya sun zabi sabuwar hukumar wucin gadi da za ta jagoranci shirya zaben gama gari a kasar a watan Disamban shekarar 2021.

An dai zabi Muhammad Yunus Al-manfy a matsayin Shugaban majalisar zartarwa na gwamnatin rikon kwaryar yayin da aka zabi Abdulhameed Dabeebah a matsayin sabon firanminista.

Wannan zaben dai ya kawo karshen mulkin tsofin jami'an gwamnatin hadakar kasar da ta kunshi Aqilah Saleh, shugaban majalisar Gabashin kasar, da Fathy Bashaga, ministan cikin gidan gwamnatin Tripoli wadanda suka sha kaye a zaben.