1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabuwar gwamnati a Kasar Lebanon

Zulaiha Abubakar
February 1, 2019

Firaministan kasar Saad al-Hariri ya kaddamar da gwamnatin hadaka wacce za ta kawo karshen matsalar durkushewar tattalin arziki da kasar ke fuskanta.

https://p.dw.com/p/3CY5t
Libanon designierter Primierminister Saad al-Hariri
Hoto: Getty Images/AFP/A. Amro

Masana a kasar sun yi hasashen cewar sabuwar majalisar zartaswar kasar wacce ta kunshi ministoci 30 daga jam'iyyin adawa za ta fusakanci kalubalen tattalin arziki kasancewar kasar wacce tafi kowacce kasa tulin bashi yanzu, tun bayan bullar rikici a kasar Siriya rashin aikin yi ya karu a Lebanon da kaso 20 tsakanin shekara ta 2011 zuwa shekara ta 2014 lamarin da ya zuwa yanzu gwamnatin ta gagara magancewa.

Kungiyar Hezbollah wacce kasar Amirka ta ayyana a matsayin kungiyar ta'adda na daga cikin wadanda mambobinta biyu suka rabauta da mukaman ministoci cikin sabuwar gwamnatin hadakar.